Ahmed Musa Ibeto

Ahmed Musa Ibeto wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar Afurka Ta-kudu yayi murabus daga mukaminsa, sannan ya sauya sheka zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

Ibeto dai shi ne tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Neja, inda ya sauka tare da Gwamna Muazu Babangida Aliyu Talban Minna a shekarar 2015. Kafin dai karewar  Gwamnatinsu ne dai Ibeto ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Inda Shugaba Buhari ya zabe shi a matsayin Minista daga jihar Neja,kafin daga bisani a maye shi da Bawa Bwari daga jihar ta Neja. Daga baya ne kuma bayan da aka janye sunansa daga matsayin Minisa, aka bashi mukamin jakadan Najeriya a kasar Afurka ta-kudu.

Wata majiya mai tsuhe ta tabbatar da cewar, Ahmed Ibeto zai tsaya neman takarar Gwamnan jihar Neja a karkashin tutar jam’iyyar PDP, inda ake sa ran zai yanki tikitin shiga jam’iyyar ta PDP a mazabarsa dake Ibeto a karamar hukumar Magama ta jihar Neja.