Home Labarai IBTILA’I: Mata ta ƙona kan ta bayan mijinta ya sake ta a Jigawa

IBTILA’I: Mata ta ƙona kan ta bayan mijinta ya sake ta a Jigawa

0
IBTILA’I: Mata ta ƙona kan ta bayan mijinta ya sake ta a Jigawa

Wata mata ‘yar shekara 40 (an sakaya sunanta) ta cinna wa kanta wuta bayan mijinta ya sake ta a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

DSP Lawan Shiisu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a Dutse, a yau Juma’a.

Shiisu ya ce matar da ke zaune a kauyen Garin Mallam ta zuba wa kan ta man fetur sannan ta banka wuta.

“A ranar Alhamis da misalin karfe 7:40 na safe, rundunar ta samu labari mai ratsa zuciya da ban tausayi na wani lamari da ya faru a Guri, wanda ya nuna cewa wata mata ƴar shekara 40 a kauyen Garin Mallam ta zuba wa kan ta man fetur ta kuma cinna wuta, inda ta kone kurmus.

An ruwaito cewa ta aikata kisan kan ne a wajen garin kauyen.

“Bayan wannan rahoton, tawagar jami’an hedikwatar ’yan sanda ta Guri sun yi tururuwa zuwa wurin inda su ka tabbatar da faruwar lamarin.

“Jami’an sun kai konannen jikin zuwa asibiti, daga baya kuma suka mika gawar ga ‘yan uwa domin yi mata jana’iza,” in ji Shiisu.

Ya bayyana cewa binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta samu damuwa ne watanni kadan bayan auren ta da mijinta ya mutu.