
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Alhassan Doguwa, ya sha alwashin ciyo wa jam’iyyar APC a zaben gwamna a 2027.
Doguwa ya bayyana haka ne a Abuja a jiya Lahadi, yayin da ya ke mayar da martani kan ikirarin da wani dan majalisar wakilai, Abdulmumini Jibrin ya yi na cewa yana barazana ga nasarar APC a jihar Kano.
Jibrin ya kuma ce Doguwa ƙajaga ne na siyasa a jam’iyyarsa ta APC.
Doguwa ya ce zai tabbatar da samun nasara ga jam’iyyar APC a zaben 2027, inda ya ce a bar shi ya zama darakta-janar na yakin neman zaben jam’iyyar a 2027 a jihar.
“Ina so in yi amfani da wannan dama domin in nuna girmamawa ga shugabannin jam’iyyarmu da su ba ni damar hada kai tare da yin aiki a matsayin D-G na yakin neman zaben Jihar Kano a 2027.
“Ni ba ƙajaga ba ne siyasa a Kano; Ni kadara ne, abin alfahari ga jam’iyyar APC a jihar da ma kasa baki daya,” inji shi.