
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshen jihar Kogi, a yau Talata ta ce hukumar ta mayar da hankali ne wajen rage yaduwar miyagun kwayoyi domin dakile amfani da su da samar da zaman lafiya.
Umar Yahuza, kwamandan hukumar na jihar ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran na Ƙasa a Lokoja.
Malam Yahuza ya bayyana cewa, idan aka samu raguwar yaduwar miyagun kwayoyi, amfani da kuma dogaro da su zai ragu, wanda a nan gaba zai rage munanan laifuka kamar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran su a cikin al’umma.
A cewarsa, shaye-shayen miyagun kwayoyi ne ke haifar da tashe-tashen hankula da sace-sacen jama’a da ke addabar al’umma a yau.
“Dukkan matsalolin tada kayar baya da kuma garkuwa da mutane sakamakon miyagun kwayoyi ne, domin ba zai yiwu a yi garkuwa da mutane ba tare da amfani da miyagun kwayoyi ba.
“Amma za mu iya dakatar da tayar da kayar baya, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka idan muka hada kai wajen yaki da matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan,” in ji shi.