Home Labarai Idan ku ka tashi aure, ku duba mai tsoron Allah da addini — Malami ya shawarci al’umma

Idan ku ka tashi aure, ku duba mai tsoron Allah da addini — Malami ya shawarci al’umma

0
Idan ku ka tashi aure, ku duba mai tsoron Allah da addini — Malami ya shawarci al’umma

Wani malamin addinin Islama, Sheikh Shuaib Agbarere, ya shawarci al’ummar musulmi da su fifita tsoron Allah da addini wajen zabar wadanda za su aura.

Agbarere ya bayar da wannan shawarar ne a jiya Lahadi a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a wajen laccar watan Ramadan da kungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society ta shirya a Abuja.

Ya yi nuni da cewa, ‘’Yana da muhimmanci ga musulmi ya auri macen da ta dukufa wajen ibada. Idan ka auri mace mai addini, ka auri mafi kyawun mace.

“Idan ka auri mace mai addini, ka auri mace mafi arziki. Don haka ku ce wa ‘ya’yanku su fifita ibada da addini yayin yin aure.

” Annabi Muhammad (SAW) ya ce ana auren mace ne saboda dalilai guda hudu: don dukiyarta, da matsayinta, da kyawunta, da addininta.

” Amma shi (Annabi Muhammad) ya yi nasiha da mu je neman mace mai addini.

Malamin ya lura cewa duk matsalolin tattalin arziki da tsaro da suka addabi kasar za a iya magance su idan ma’aurata suka auri waɗanda su ka cancanta.