
Babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, IGP Alkali Usman ya mayar da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Abubakar Lawal, zuwa jihar Ebonyi, biyo bayan zarge-zargen cin hanci da wasu manyan ƴan yan sandan jihar ke yi a kansa.
A wata takardar sanarwa mai lamba: TH.5361/FS/FHQ/ABJ/V.T3/87 da aka saki da yammacin Juma’a, IGP ɗin ya tura kwamishinan ƴan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba domin ya maye gurbin Lawan nan take.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa manyan jami’an ƴan sanda a rundunar ƴan sandan jihar Kano sun koka kan yadda CP ɗin ke aikata ayyukan cin hanci da rashawa, lamarin da ya sa IGP ya bayar da umarnin gudanar da bincike na ƙarƙashin ƙasa a kan zargin.
A cewar wasu majiyoyi na cikin gida, Lawan, wanda aka kawo shi Kano a watan Agusta, sai ya dawo da dukkanin “korafe-korafe da za a samu kuɗi ” zuwa ofishinsa da kuma sanya wa wasu ɓangarori haraji na mako-mako.
Shi kuma sabon kwamishinan yan sandan da s ka kawo Kano ya kammala karatun digiri a fannin tarihi a Jami’ar Sakkwato, kuma ya yi digiri na biyu a fannin shari’a da diflomasiyya a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Port-Harcourt, Jihar Ribas.
Ya shiga aikin ‘yan sandan Nijeriya a 1990 a matsayin mataimakin Sufeto na ‘yan sanda, Cadet ASP, a makarantar horon‘yan sanda a Jihar Kaduna, inda ya dauki horo na tsawon watanni 18 sannan aka tura shi rundunar ‘yan sandan jihar Oyo a matsayi me aiki a ɓangaren gudanar da ayyuka.
Daga nan kuma sai aka mayar da shi Rundunar ƴan sanda a Jihar Neja a shekarar 1992 inda ya zama dogari ga Gwamnan Jihar Neja a lokacin, Musa Inuwa.