
Ijeoma Nwaogwugwu, Manajan Darakta ta Arise TV, ta yi murabus.
An jiyo cewa Nwaogwugwu, fitacciyar yar jarida, ta yi murabus a jiya Laraba bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Majiyoyin da suka tabbatar da murabus din nata a yau Alhamis ba su bayyana dalilin da ya sa ta yanke wannan shawarar ba.
Nwaogwugwu ta kasance babbar edita a rukunin jaridun Thisday.
Ita ce Editan Kasuwanci na rukunin, inda daga bisani ta tashi ta zama Editan jaridar Asabar, Lahadi kuma a ƙarshe Editan Daily, ma’ana wacce ta ke fito wa a ranakun aiki.
Gabaɗaya, ta kasance Edita tsawon shekaru 11.