Home Labarai Ina fargabar rayuwa ta, in ji ɗan jaridar da ya bankaɗo badaƙalar Digiri ɗan Kwatano

Ina fargabar rayuwa ta, in ji ɗan jaridar da ya bankaɗo badaƙalar Digiri ɗan Kwatano

0
Ina fargabar rayuwa ta, in ji ɗan jaridar da ya bankaɗo badaƙalar Digiri ɗan Kwatano

Wani dan jarida mai binciken ƙwaƙwaf a Najeriya, Umar Audu, ya bayyana cewa ya damu da tsaron lafiyarsa sakamakon rahoton binciken da ya gudanar a baya-bayan nan, wanda ya bankado wata badakalar kwallon digiri a kasashen Togo da Jamhuriyar Benin.

Idan ba a manta ba, dan jaridar , wakilin jaridar Daily Nigerian, ya ruwaito kwanan nan cewa ya samu shaidar digiri a cikin makonni shida da shigarsa daya daga cikin irin wadannan jami’o’in, sannan da shi aka yi shirin yi wa kasa hidima na NYSC.

Dan jaridar da a yanzu haka ke boye, ya bayyana cewa ya samu duka kwafi na shaidar digiri a jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, Cotonou, Jamhuriyar Benin a makonni shida kacal.

A wata hira da gidan Talabijin na Channels a jiya Laraba, ya bayyana cewa yana cikin damuwa cewa tsarin tsaro a Najeriya bai baiwa ‘yan jarida kwarin gwiwar yin aikinsu ba tare da fargabar cin zarafi ba.

Da mai gabatar da shirin ya tambaye shi ko ya samu wata barazana bayan rahoton nasa, Audu ya bayyana cewa duk da cewa har yanzu bai samu wata barazana ba, amma dai yana wata maɓoya saboda yana bukatar ba da fifiko ga tsaron lafiyarsa.

“Akwai damuwa da yawa daga abokai da ‘yan uwa game da tsaron lafiya ta da rai na. Sun damu kwarai da gaske, kuma a matsayina na dan jarida, na yi imanin ya kamata a bar ni na gudanar da aikina ba tare da wata barazana ba.

“Wannan lamarin ya bayyana irin al’ummar da muke rayuwa a ciki, inda ya kamata ‘yan jarida su rika gudanar da ayyukansu cikin lumana da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu.

“Ina so in yi amfani da wannan dandali domin yin kira ga hukumomi da su tabbatar da kariya ta, duk da cewa a halin yanzu ina cikin wani wuri mai tsaro. Duk da haka, ba ni da tabbas game da abin da zai iya faruwa nan gaba, saboda ina ta amsa tambayoyi kuma rahoton nawa ya shiga duniya duk da cewa har yanzu ban fuskanci wata barazana ba,” in ji shi.