
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda alkalan kotun koli za su iya tabbatar da adalci kan karar zaben gwamnan jihar da ke gaban kotun.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Yusuf ya baiyana hakan ne a filin wasa na Sani Abacha a jiya Lahadi, yayin bikin kaddamar da rundunar jami’an tsaro 2,500 da makarantar horas da jami’an tsaro za ta horas da su a Kano.
“Muna da yakinin cewa alkalan kotun koli za su yi mana adalci ga daukaka karar da ke gabansu, don haka mutanen Kano su kwantar da hankalinsu,” inji shi.
Ya bayyana cewa an kafa makarantar horar da jami’an tsaron ne a zamanin gwamnatin Rabi’u Kwankwaso da nufin horas da matasa kan harkokin tsaro.
“An zabo wadanda aka horas da su ne daga kananan hukumomi 44 na jihar, kuma za a dauke su aiki tare da tura su ga ma’aikatun gwamnati daban-daban da zarar sun kammala daukar horon.
Gwamna Yusuf ya yaba da goyon bayan da mazauna Kano suke ba su, ya kuma bukace su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da son zaman lafiya.
“Ina so in tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatina za ta ci gaba da samar da tsare-tsare na ci gaban al’umma da za su tallafa wa matasan jihar.
A cewar sa, wadanda suka ci gajiyar shirin za a samar musu da ayyukan yi a ma’aikatu na jiha da kuma kananan hukumomi 44.