
Sakataren Ƙungiyar Dillalan Man Fetur mai Zaman Kan ta ta Ƙasa, IPMAN, James Tor, ya dora alhakin wahalar man fetur fa ake fama da ita a ƙasar nan kan rikicin Iran da Isra’ila.
Da ya ke tsokaci kan lamarin a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE, Tor ya bayyana irin rawar da gwamnatin tarayya ke takawa wajen shigo da man fetur da kuma ware su ga masu ruwa da tsaki ciki har da IPMAN domin rabawa.
Ya yi nuni da cewa, tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya a halin yanzu, sun kara ta’azzara tabarbarewar yanayin da ake fuskanta, wanda ya haifar da cikas a harkar samar da man fetur din.
Sai dai ya ce hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa (NNPC) ta kara himma wajen ganin an shawo kan lamarin ta hanyar bude gidajen man fetur domin tabbatar da samar da shi.
Ya ce, “Gwamnatin Taraiya ce mai shigo da man fetur a kasar nan. Kuma idan sun shigo da wadannan shi sai su ba mu masu ruwa da tsaki (wanda IPMAN na daya daga ciki) don rabawa. Don haka abin da muke samu ne za mu iya bayarwa. Idan babu man, to ba za mu iya ba da wani abu ba.
“Shugaban kungiyar IPMAN ya kira ni tun da fari ya sanar da ni karin man da ake samu. Don haka abin da muke gani ba shi muka yi tsammani ba.
“Kuma me ke faruwa? Ka ga, rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya. Rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran kuma yana shafar rabon mai. Duk wadannan abubuwa idan aka hada su waje daya, suna shafar samarwa da rarraba albarkatun man fetur.