26.8 C
Abuja
Friday, July 1, 2022

Ƴan IPOB sun fille kan ɗan majalisa a Anambra

Must read

 

 

Wasu ƴan bindiga da a ke kyautata zaton ƴan haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne sun cire kan wani ɗan majalisar dokokin Jihar Anambra, Dakta Okechukwu Okoye, bayan sun yi garkuwa da shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindigan su ka sace ɗan majalisar da ake kira “Okey Di Okay” da ke wakiltar Aguata ta arewa, mazaɓar gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Chukwuma Soludo.

Bayanai sun ce an tsinci kan ne da aka fille a gefen hanya tare da wata wasiƙa a yankin Amichi a Anambra.

Rundunar ƴan sandan Anambra cikin wata sanarwa game da al’amarin ta ce a yayin gudanar da bincike wasu mutane sun tsinci gawar mutum ba kai, wanda aka tantance gawar ɗan majalisar ce Hon Okechukwu Okoye.

thisday nigeria news

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article