
Wata kungiyar siyasa da zamantakewar al’ummar jihar Delta mai suna ‘Ndokwa Renaissance Group’, ta yi barazanar haɗa kan al’ummar yankin Sanatan Delta ta Arewa domin yiwa Sanata Ned Nwoko da ke wakiltar su a majalisar dattawa kiranye.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a Abuja.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Hon. Chinedu Egbenumolise, da sakatare, Dokta Uti Onyeukwu, sun yi kakkausar suka ga kalaman Sanata Nwoko a kwanan baya a zauren majalisar dattawa, inda ya yi kira da a samar da jihar Anioma kuma a yanko ta daga ɓangaren Delta ta Kudu maso Kudu, a kuma kai ta Shiyyar zuwa Kudu maso Gabas a matsayin wani mataki na ganin cewa ba a maida yankin yankin saniyar-ware ba.
Kungiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa Sanata Nwoko zai gabatar da irin wannan kudurin ba tare da tuntubar mutanen yankin Delta ta Arewa ba, wadanda hakan zai iya yi musu illa.
Sun yi barazanar kai dan majalisar tarayyar zuwa kotu idan har bai janye kalaman nasa ba, suna masu bayyana hakan a matsayin mai hatsarin gaske da son kai, rashin bin tsarin dimokradiyya, da kuma rashin bin tsarin mulkin kasa.