Home Labarai Isra’ila ta kashe wani ƙusa a ƙungiyar Hamas

Isra’ila ta kashe wani ƙusa a ƙungiyar Hamas

0
Isra’ila ta kashe wani ƙusa a ƙungiyar Hamas

Kungiyar Hamas ta sanar da kisan da Isra’ila ta yi wa mataimakin shugabanta, Saleh al-Aruri a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon.

Wani babban jami’in tsaro a Beirut ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, an kashe Aruri da wasu masu tsaronsa ne a wani hari da Isra’ila ta kaddamar a yankin wajen kudancin Beirut da ke zama kakkarfar tungar mayakan Hezbollah mai kawance da Hamas.

Tuni Firaministan Lebanon, Najib Mikati ya yi tur da kisan da aka yi wa Aruri, yana mai bayyana harin a matsayin wata manufa ta janyo Lebanon gadan-gadan cikin yakin Isra’ila da Hamas.

Da yammacin wannan Talatar ce aka ji karar wata fashewa a birnin na Beirut, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba a yayin da wasu hotunan da aka watsa ta shafukan sada zumunta ke nuna irin barnar da tashin gobarar ya h koaifar.

Harin na zuwa ne bayan Kungiyar Agaji ta Red Cross a Falasdinu ta ce, an kashe mutane da dama tare da raunata wasu a wani hari da Isra’ila ta kai shalkwatar birnin Khan Younis da ke Gaza.

A bangare guda, Isra’ila ta ce, dakarunta sun kashe gomman ‘yan tawaye a arewacin Zirin Gaza a jiya Litinin, a yayin da jirgin yakinta da tankoki suka zafafa hare-hare a yankin kudancin birnin na Gaza.

Rfi