
Iyalan fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, sun ƙaryata rahotannin da su ka ce ba su da tushe balle makama da aka yada cewar malamin ya rasu.
A safiyar yau Laraba ne aka fitar da jita-jitar cewa Sheikh Dahiru Bauchi, wanda yana daya daga cikin jagororin Darikar Sufanci ta Tijjaniyya a Najeriya ga rasu.
Sai dai kuma a wani martani na gaggawa, Sanusi Dahiru, dan gidan malamin, ya ce, “dan shekaru 97 malamin yana nan lafaiya kalau.
“Mun yi magana da shi kuma yana cikin koshin lafiya a Abuja da safiyar yau.
“Sheikh Dahiru-Bauchi zai bar Abuja zuwa Kaduna gobe (Alhamis) domin rufe Tafsirin Alkur’ani na shekara-shekara, inda ya samu wakilcin dansa, Dakta Sulumbai Dahiru.
“Don haka jama’a a su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa Sheikh Dahiru Usman-Bauchi ya rasu.
“Har yanzu yana raye tare da koshin lafiya duk da tsufa”, kuma ya bukaci musulmai masu aminci da su yi addu’a don samun lafiya ga malamin.