KanarSambo Dasuki mai ritaya

Tsohon dogarin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Almustapha Haruna Jakolo, ya bayyana yadda tsohon mai baiwa tsohon  Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, a zamanin mulkin soja a shekarar 1983 bayan juyin mulkin da aka yi, Sambo ya nada Buhari a matsayin Shugaban kasar Soja a wancan lokacin.

Mista Jokolo wanda shi ne tsohon Sarkin Gwandu da aka sauke, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Sun, yana mai mayar da martani kan wani littafi da Janar Muhammadu Iliyasu Bashar Sarkin Gwandu wanda ya gaji Jakolo ya wallafa.

A cewar  tsohon Sarkin Gwandu, Kanar Sambo Dasuki ya taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da kudi a juyin mulkin da ya kawo Buhari kan karagar mulki a shekarar 1983, bayan da aka kifar da Gwamnati Shehu Shagari.

Jakolo yake cewa “Zance na gaskiya, zuciyata tana bugawa, hankali na yana tashi matuka idan na kalli yadda ake yiwa Sambo Dasuki, na kan yi mamaki ainun”

“Abin mamaki ne kwarai da gaske. Idan har ban bayyana irin rawarda Sambo Dasuki ya taka ba a juyin mulkin shekarar1983, idan ba dan Sambo Dasuki ba, Buhari ba zai taba zama Shugaban kasa ba a wancan lokacin”

“Sambo shi ne mutumin da ya gamsar da mutane kan nadin Buhari a matsayin Shugaban kasa a wancan lokacin. Na rantse da Allah, na kuma rantsewa cewa, shi ne (Sambo Dasuki) ya kwantar da hankalin mutane kan nadin Buhari a matsayin Shugaban kasa. Lokacin da muke shirya juyin mulkin da ta sanadinsa Buhari ya zama Shugaban kasa,Sambo Dasuki ne ya samar da dukkan kudaden da aka yi amfani da su wajen juyin mulkin”

“A wancan lokacin Sambo Dasuki ya samo kudaden da aka yi juyin mulkin daga wajen Janar Aliyu Gusau da kuma Shugaban hafsan soja na wancan lokacin domin shirya juyinmulkin, babu sisin kwabo da aka karba a wajen Buhari akan juyin mulkin da ya bashi damar zama Shugaban kasa”

“Bama wannan kadai ba, Sambo Dasuki yayi amfani da kudin mahaifinsa, ya dauki nauyin wasu Malamai domin su tafi kasar Saudiyya su yi adduah,akan Allah yasa a yi wannan juyin mulki cikin nasara” A cewar Mista Jakolo.

Da yake bayani a cikin littafin da ya wallafa, ya ce “haduwa ta da gogaggen dan leken asiri” Wanda Yusha’u Shuaib ya wallafa, yace Sambo Dasuki ya yi bayani dalla-dalla akan yadda shi (Sambo) tare da wasu sojoji guda biyu, suka samu Buhari kan batun juyin mulkin 1983.

Mista Dasuki, ya bayyana cewar “shi ne tare da gudunmawar wasu sojoji guda biyu (Manjo Mustapha Jakolo da manjo Lawal Gwadabe) muka tafi Jos domin mu shaidawa janar Buhari a lokacin yana rike da mukamin GOC mai lyra da bataliya ta uku, muka shaida masa kudurin yin juyin mulkin 1983, wanda sanadinsa ne ya zama Shugaban kasa, Buhari shi ne mutumin da yafi kowa cin moriyar juyin mulkin da aka yiwa Shagari”.

Haka kuma, Mista Dasuki, ya cigaba da cewar, Buhari ya nuna tirjewarsa da kuma nuna rashin jindadin kan abinda ake yunkurin yi, amma muka gamsarda shi cewar babu wani abun damuwa, “Karka ji komai tunda a hannun ‘yan Siyasa zamu karbi mulki babu wani abu da zai faru”

A lokacin da Shuaibu, mawallafin wancan littafi, ya tambayi Sambo Dasuki, me ya sanya shi sanya hannu a juyin mulkin da aka yiwa Mista Buhari, shekara biyu bayan sun jagorancin juyin mulkin da ya kawi Buhari a matsayin Shugaban kasa, Mista Dasuki ya bashi amsa da cewar, “Buhari shi yafi kowa sanin wanda zai zarga kan wannan batu.”

Sambo Dasuki ya cigaba da cewar “A koda yaushe ina girmama wadan da suke sama da ni a tsarin aikin soja, ko muna soja ko mun yi ritaya, ina girmama su. Duk da cewar ni karamin soja ne, amma ina daga cikin wadan da suka tsare Buhari, amma ba ni na kama shi ba.

“Na samu Buhari ne lokacin da ake tsare da shi a sansanin soja dake Bonny tare da Lawal Rafindadi. Babu ta yadda za’a yi ace na musguna masa a wancan lokacin,kamar yadda wasu ke fadi. Amma na godewa Allah, kusan duk wanda aka yi wannan al’amari da su suna nan a raye”

Dan haka ba gaskiya bane, zargin da ake yi cewar, Sambo Dasuki shi ne jagoran sojojin da suka kama tare da tsare Buhari a juyin mulkin da aka yi masa shekarar 1985, Kanar Abdulmumini Aminu, wani dan asalin jihar Katsina, ya bayyana sunayen mutane sukun da suka tsare Buhari a wancan lokacin, a wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Sunday Trust a watan Agustan 2015 zaku iya karanta tattaunawar ta wannan rariya likau da zaku iya samu a (Links: https://goo.gl/KEz5nkhttps://goo.gl/wirj2Thttps://goo.gl/9vZM5A).

Kanar Aminu yace,mutum uku ne suka jagoranci tsare Shugaban kasar wancan lokacin (Janar Buhari) wanda suka hada da Lawal gwadabe da John Madaki.

Ya karada cewar “Ba zan ji shakkar bayyanawa duniya cewar ni ne na jagoranci tsare Shugaban kasar wancan lokacin Janar Buhari. Na tafi Dodan Barak a wancan lokacin tare da rakiyar sojoji guda biyu Manjo John Madaki da Lawan Gwadabe, mu uku ne muka isa inda Shugaban kasa yake, nine wanda na hau kan bene na sauko da Buhari.

“Tareda dukkan girmamawa, Ina yawan karantawa a shafukan jaridu,mutane suna cewar wai mun cusguna masa, mun kuma ci zarafinsa. Wannan sam ba gaskiya bane. Ni da janar Buhari, mu biyu ne kadai muka san abinda yafaru da shi, dan haka babu wani abu mai kama da cin zarafi da na yi masa”

“Mun bashi dukkan girmamawa a matsayinsa na Shugaban kasa, tun kafin wannan lokacin ma, muna matukar girmamashi, saboda yanayinsa. Muna girmamashi har ya zuwa wannan lokaci, babu kuma wani sabani tsakaninmu da shi, shi kansa ya san cewar ba yadda muka iya a wancan lokacin aikin soja ne ya biyo ta kansa”

“Shi da kansa ya taba shaida min a wani lokaci cewar, batu ne kawai na waye zai zama Shugaban kasa lokacin da ake tsananin adawa da mulkin Shagari. Ina daya daga cikin wadan da suka taka muhimmiyar rawa wajen kawo shi kan mulki.”