Home Labarai JAMB ta kara kuɗin fom

JAMB ta kara kuɗin fom

0
JAMB ta kara kuɗin fom

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta kara kudin rajistar jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, UTME, ta 2024 da ke tafe, UTME, inda ta kuma sanar da bude shafin yin rajista na yanar gizo don saka bayanan masu yin rijista.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a jiya Lahadi, hukumar ta ce wadanda za su zana jarabawar ta gwaji za su biya Naira dubu 7,700, yayin da wadanda ba su da sha’awar zana jarabawar gwajin za su biya Naora dubu 6,200.

Sai dai jaridar DAILY NIGERIAN ta lura da karin Naira 2,100 a cikin kudin jarabawar bana domin a shekarar da ta gabata wadanda suka zana jarabawar sun biya Naira 5,600 ne kacal.

Sanarwar ta ce: “Muna masu sanar da duk masu neman jarrabawar UTME/DE ta 2024 cewa an bude shafin bayar da bayanai na masu son zama jarrabawar a hukumance, yayin da za a fara siyar da gubdarin don din a ranar Litinin 15 ga Janairu, 2024.

“Don haka, yana da muhimmanci ku kiyaye ranakun da za a zana jarabawar UTME/DE mai zuwa: