Home Labarai Jami’an NSCDC sun kama matashi bisa kashe mahaifinsa a Kano

Jami’an NSCDC sun kama matashi bisa kashe mahaifinsa a Kano

0
Jami’an NSCDC sun kama matashi bisa kashe mahaifinsa a Kano

Hukumar tsaron faran hula ta ƙasa, NSCDC, wacce aka fi sani da ‘Civil Defence’, reshen jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Alkasim Ya’u da laifin daɓa wa mahaifinsa wuka har lahira a Tudun Yola ‘C’ dake karamar hukumar Gwale a jihar.

Kwamandan hukumar NSCDC, Mohammed Falala ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa ta wayar tarho a Kano a yau Lahadi.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 11 na darw a gidan wani Salisu Bala.

“Mahaifin marigayin, Alhaji Ya’u Mohammed, ya kawo dansa ne mai cutar tabin hankali, Alkasim Ya’u, zuwa asibitin mahaukata na Dawanau, domin a duba shi, inda suka kafa layin ganin likita a ranar Asabar, 6 ga watan Janairu,”

Ya bayyana cewa, maimakon ya koma Katsina, sai marigayin ya yanke shawarar kwana a gidan dan uwansa a nan Tudun Yola ‘C’.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa alkasim ya kamu da tabin hankali ne sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyi.

“A lokacin da suka isa Tudun Yola, sai Alkasim ya dauki wani abu mai kaifi ya raunata mahaifin, har sai da jami’an NSCDC da ke yankin suka shiga tsakani suka kai wanda abin ya shafa asibiti suka kama wanda ake zargin,” inji shi.

Ya ce tuni ‘yan uwa suka fara shirye-shiryen mayar da gawar zuwa Katsina domin yi masa jana’iza, yayin da aka mika wanda ake zargin ga ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki domin faɗaɗa bincike.