
Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, na daya daga cikin mutane shida da za a ba su lambar yabo ta digirin girmamawa a jami’ar Oxford.
Sauran wadanda za a karrama sun hada da Warren East, Sir Demis Hassabis, Sir Michael Palin, Anoushka Shankar da Farfesa Salim Yusuf.
Za a ba su duka lambar digirin girmamawa a ranar Laraba, 19 ga Yuni, 2024.
Okonjo-Iweala, kwararriya a fannin tattalin arziki, ita ce Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya ta bakwai.
Ta fara aiki ne a 2021, inda ta zama mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da ta rike wannan mukami.
A 2022, Dokta Okonjo-Iweala ta samu lambar girma ta gwamnatin taraiya ta babbar kwamandan odar Niger (GCON), wanda itace mafi girma ta biyu a lambobin girma a Najeriya.
A halin yanzu tana aiki a kwamitin amintattu na dandalin tattalin arzikin duniya kuma tana jagorantar hukumar kula da tattalin arzikin ruwa ta duniya.
A baya dai, ta taba rike mukamin ministar kudi ta Najeriya, inda ta rike mukamin na tsawon shekaru bakwai a cikin wa’adi biyu, sannan ta rike mukamin ministar harkokin waje na dan lokaci.