Shugabar Jami'ar Dutse Farfesa Fatima Batoul Mukhtar

Daga Abba Wada Gwale

Hukumar kula da harkokin jamio’in ƙasarnan ta NUC ta baiwa Jami’ar Tarayya da ke garin Dutse wato Federal University, Dutse (FUD) izinin fara koyarda aikin likitanci.

Wannan karatu za’a fara shi ne a shekarar karatun 2017/2018

Sanarwar da magatakardar jami’ar Bukar Usman ya fitar a ranar Lahadin yau ta yi nuni da cewa fannin karatu guda biyar (dake alaƙa da juna) da ke kwalegin horar da aikin likitancin aka bada izinin yi.

Magatakarda Bukar ƙara da cewa fannonin karatun English da Biology da Physics da Political Science da Zoology da Botany da Chemistry su hukamar ta sahalewa jami’ar yi.

Fannin Computer Science da Biotechnology kuwa izinin talala aka basu.