Daga Hafizu Murtala

Kowa zai yarda dani cewa a ýan watannin da suka shude Siyasar Nigeria kamar yadda aka saba ta fara daukar zafi, wannan ya hada da rikicin majalisun tarayya da kuma sauye sauyen sheka da shugabannin siyasa suke yi daga wata jamíyya zuwa wata saboda muna dab da zaben 2019.

Wannan ya saka magoya bayan wadannan Jagororin suna ta musayar yawu a fagen kafofin sada zumunta. Masu suka nayi, Masu yabo nayi, Masu Zagi nayi da sauransu.

Sabo da takaici nace wa kaina, bazan kara Maganar siyasa da kowa ba a kafar sada zumunta ko a wajen ta, zan rike raáyi na na siyasa a zuciya, ranar zabe idan da hali na zabi abinda raina yake so. Amma bayan Nazari da bibiyar mutane masu hangen nesa ta tabbata cewa idan mutum zai kiyaye cin mutuncin dan uwansa, babu laifi don ka baiyana raáyinsa aka akan wani abu da alúmma take tattaunawa akai. Amma akwai wanda yace dani ai ita Siyasa, babu wani amana ko mutunci a cikinta. Wannan zancen ba gaskia bane.

A Khudubarsa ta yau, Limamin Masallacin Jumaá na Area 10 dake Abuja As-Sheikh Al-Yolawiy yayi nasiha akan musulmi suyi duba akan makasudin zamantakewa da ýanuwantaka ta musulunci, su guji gaba, aibatawa, kiyayayya da sauransu saboda raáyi na Siyasa. Ya kawo Ayoyi da dama a Al-Qurani mai tsarki ta yadda Allah yake umartarmu damu zama Alumma daya, masu son juna da

Wannan Khudubah ta sosa min wajen da ke min kaikayi, bisa nazarin da nayi akan yadda alúmma suka hasala suna ta jifan juna da maganganu na rashin dacewa saboda raáyi na siyasa. Raáyin da na lura yana da matsala a rayuwarmu. Dalilin fadin hakan kuwa shina, yawancin mutanen mu za kaga suna son Jagororin su kawai saboda su biya bukatar zuciyar su, da kona zuciyar abokan adawar su, amma ba wai don su samu wani abu a wajen wadannan Jagororin ba, ko su amfana dasu ta wata hanyar. Domin idan don aikin da Shugaba ya keyi kake son sa, to ka sani wannan aikin da yayi ba kai kadai zai amfana ba, duk wani mai rayuwa a wajen da aka yi aikin zai amfana dashi.

Wannan yasa nake tunanin son da wasu suke yiwa Shugabanni yayi kama da abinda Bature yake cewa “addiction” ta yadda wani zai ci Goro, Ko busa Sigari, don samun kwanciyar hankali da nutsuwa. Iyakar kenan. Yawancin wadannan magoya bayan, basu damu dasu suyi musabiha da shugabansu ba, ko yasan dasu, ko su kai masa ziyara, amma fa kai da kuke faduwa ku tashi tare zai iya gaba da kai akan wannan Shugaban, kaga kuwa akwai matsala babba.

Na lura da yadda ake yada Karya, Kazafi, Sharri a kafar sadawarwar zamani, saboda biyan bukatar zuciya. Wasu za kaga suna da gwani, wanda akansa sai inda karfinsu ya kare, wasu kuma haka kawai suka dauki karan tsana suka dorawa wani shugaba, aikinsu kullum shine yada maganganu na batanci akan sa. To mu sani, Allah yace duka abinda ka fadi ko ka yada, akwai Malaïka da yake rubutuwa, kuma za kayi bayani a gaba.

Dan gane da ýan Siyasa kuwa, wannan hoton ya ishe mu misali, su kam babu abinda ya dame su, duk abinda zai kawo masu mafita a siyasar su, shi suke bi, kadan ne suke tuntubar magoya bayansu kafin su dauki wani mataki na siyasa. Yawancin wadanda muke kaunar ma, idan suka suka samu mukamin, ýaýansu da surukansu da makusantan su, sune suke morewa fiye damu da muke gaba da junan mu akan su.

Ga kuma yan siyasa wani lokacin akwai abun haushi duba da yadda kusan sama da mutane goma suka fito duka daga yanki daya a PDP suke neman kujerar shugaban kasar da wanda yake kai ma yake nema, kuma yana da magoya baya, da ýan sanda, da soja da sauransu.

Shi Mulkin nan dai Allah ke bada shi, yasan wanda zai bawa 2019, ko muso ko kada muso. Don haka idan muna sane da wannan menene na tada jijiyar wuya? Muna sane a tarihin kasar nan, akwai manyan mutanen da sun nemi mulkin nan kamar ransu zai fita, amma Allah bai ga dama ya basu ba. Haka da yawansu suka mutu ba tare da samun biyan bukar su ba.

A karshe mu sani, koma dai menene, mulkin Nigeria zai bar Arewa ya koma Kudu bayan zangon da zamu shiga ya kare, kuma shekara takwas za suyi suna yi, a wannan yarjejeniyar da Idan suka ga dama ma suna iya karya ta. A yanzu idan muka lura mutanen Kudu basu ma damu da maganar wani 2019 ba, tunda a wajen su, lokacin Arewa ne, Saboda haka muje muci kanmu.

Sannan mu sani, idan dai har dimokradiyya muke yi, to kowa ma yana da yancin ya fito ya nemi takara, don haka idan ka zage shi ko ka bata shi, to ka rage masa zunubi ka dorawa kanka. Idan baka sonsa, sai ka bari ranar zabe ka zabi Wani sa. Duniya ma dai kowa zai bar ta, balle wani mulki. Allah yasa mu dace.

HAFIZU MURTALA,
Abuja, Nigeria.