Home Labarai Janar din sojin ƙasa 113 sun yi ritaya a Nijeriya

Janar din sojin ƙasa 113 sun yi ritaya a Nijeriya

0
Janar din sojin ƙasa 113 sun yi ritaya a Nijeriya

Janaral dari da goma sha uku na sojojin ƙasa ne a Najeriya su ka yi ritaya ko kuma za su yi ritaya daga aikin a wannan shekara.

Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yaba musu kan sadaukar da rayuwar su da suka yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Ministan ya kuma ba su tabbacin biyansu hakkokinsu na fansho cikin gaggawa.

Badaru ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya Talata yayin wani taron liyafa da aka shirya musu domin karrama manyan hafsoshin da suka yi ritaya da kuma masu ritaya a Asokoro, Abuja.

Wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce wadanda aka karrama sun hada da Janar daya, Laftanar Janar daya, Manjo Janar 67 da Birgediya Janar 44, wadanda suka yi ritaya daga aikin.

Ministan ya bukaci wadanda suka yi ritayar da su yi tunani yadda ya kamata a kan mataki na gaba na rayuwa, tare da ba su tabbacin kudirin Gwamnati na gaggauta biyan fansho na ma’aikatan da suka yi ritaya.