Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN,  ya ruwaito cewar, asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya bayyana cewar kimanin yara 20,210 aka haifa a ranar farko ta wannan shekarar 2018 a Najeriya.

Wadannan sabbin jarirai na tabbatar da cewar Najeriya ce kasa ta uku a duniya da aka fi yawan samun haihuwa a duniya a wannan sabuwar Shekarar ta 2018.