Daga Hassan Y.A. Malik

Budurwan nan mai shekaru 26 da haihuwa ‘yar asalin kasar Burtaniya kuma dalibar kwaleji, Jasmin, da ta sanya budurcinta a kasuwa a fitaccen kafar saye-da-sayarwar budurci ta yanar gizo wato CINDERELLA ESCORT, a karshe dai ta samu wani jarumin masana’antar shirya finafinai na Hollywood da ya biya kudi wuri na gugan wuri yuro miliyan 1.2 (€1.2) daidai da dalar Amurka miliyan 1.48  ($1,482,528) daidai da Nairar Nijeriya miliyan 606.

Jasmin, wacce ke zaune a birnin London ta bayyana a shafukan farko na jaridun Burtaniya bisa kasa budurcinta da ta yi a kasuwa ga mai bukata, inda ta bayyana cewa za ta yi amfani da kudaden da ta samu daga hada-hadar wajen jan jari.

Ta ce ta gwammace ta karbi kudi a raba ta da budurcinta da ta bayar da shi a banza tunda ta gaji da jiran mijin da za ta amince ta bashi rayuwarta a matsayin miji.
Jarumin finafinan (an boye sunansa) wanda dan asalin jihar Los Angeles na Amurka ne ya yi nasarar samun wannan dama na kawar da budurcin Jasmin ne bayan ya kayar da abokan kararwarsa biyu, wani dan kasuwa daga birnin Munich na kasar Jamus da kuma dan wasan kwallon kafa da ke buga Firimiya Lig din Ingila.

Jasmin ta bayyana cewa iyayenta sun goya mata baya a wannan harkar ta cinikayyar budurcinta kuma sun yi murna da hukuncin da ta yanke.

“Shekaruna 26 da haihuwa, a saboda haka ina da ‘yancin zabar duk yadda na so na yi da jikina. Ban taba tsammanin farashin budurcina zai kai haka ba. Na yi matukar mamaki da farashin da jarumin ya bani,” inji Jasmin.