Home Labarai Jinkirin samun lamuni ne ya kawo tsaikon ayyukan layin dogo na Abuja-Kano da Fatakwal –Maiduguri — Minista

Jinkirin samun lamuni ne ya kawo tsaikon ayyukan layin dogo na Abuja-Kano da Fatakwal –Maiduguri — Minista

0
Jinkirin samun lamuni ne ya kawo tsaikon ayyukan layin dogo na Abuja-Kano da Fatakwal –Maiduguri — Minista
Ma’aikatar Sufuri ta Ƙasa ta ce aikin gina layin dogo na Abuja-Kano da Fatakwal-Maiduguri na fuskantar tsaiko ne sakamakon jinkirin da gwamnatin tarayya ta samu wajen samun lamuni na kashi 85 cikin 100 na kasashen waje da ake nufii yin aikin da su.
Ministan Sufuri, Mua’zu sambo me ya bayyana haka a lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai a jiya Juma’a a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya rawaito cewa, ana sa ran rancen kashi 85 cikin 100 na aikin layin dogo zai fito ne daga hannun masu kudin kasar Sin.
A cewarsa, ayyukan da su ke gudana, ana gudanar da su ne ta hanyar kuɗaɗen kasafi.
Ya ce, “Ayyukan layin dogo na Abuja-Kano da Fatakwal- Maiduguri na ci gaba da gudana amma akwai kalubale na rancen kashi 85 na kasashen waje da har yanzu ba a samu ba.
“Mun gudanar da wadannan ayyuka guda biyu ne ta hanyar kason kudi kawai, wanda ke cikin kashi 15 cikin 100 da ya kamata Nijeriya ta bayar.
“Hakika zan iya gaya muku cewa dangane da layin dogo na Kaduna zuwa Kano mun biya wa dan kwangilar aikin kashi 15 cikin 100 daga aljihun gwamnatin tarayya.
“Har sai mun sami kashi 85 cikin 100 na aikin, dole ne a ci gaba da ba da kuɗaɗen aikin ta hanyar aljihun gwamnati.”