Home Labarai Jirgin rundunar sojin sama ya faɗo amma direban ya sha

Jirgin rundunar sojin sama ya faɗo amma direban ya sha

0
Jirgin rundunar sojin sama ya faɗo amma direban ya sha

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ya yi haɗari da sanyin safiyar yau Litinin a kauyen Tami da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe, wanda ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Jirgin ya gamu da matsala ne ya na tsaka da shawagi na yau da kullum , ya fuskanci wanda ya haifar da haɗarin, inda matukin jirgin ya yi nasarar aiwatar da ka’idojin gaggawa yadda ya kamata sannan ya tsira ba tare da ya rasa rai ko Ni rauni a haɗarin ba.

Shaidun gani da ido a wurin sun ce matukin jirgin ya fito ne daga jirgin ba tare da ya jikkata ba.

Daily Trust ta tattaro cewa jama’ar kauyen na Tami sun yi gaggawar zuwa wurin da hadarin ya afku, inda suka ba da taimako tare da bayyana jin dadinsu da cewa ba a samu asarar rai ba.

Har zuwa lokacin da Daily Trust ta haɗa rahoton rundunar sojin saman Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.

Sai dai kuma ta ce Alaere Eyinimiere Obidake, jami’in hulda da jama’a na rundunar horas da jiragen sama ta NAF, Kaduna, bai samu amsa kiran da jaridar ta yi masa ba.