Home Labarai JNI ta biya wa ɗalibai 6,000 kuɗin makaranta a Bauchi

JNI ta biya wa ɗalibai 6,000 kuɗin makaranta a Bauchi

0
JNI ta biya wa ɗalibai 6,000 kuɗin makaranta a Bauchi

Kungiyar Agaji ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen jihar Bauchi, ta biya kudaden makaranta ga fiye da ɗalibai 6,000 da suka daina zuwa makaranta domin samun damar ci gaba da karatunsu a makarantu daban-daban a jihar.

Kungiyar ta kuma bayar da gudunmuwar jini ga majinyata a asibitoci, tare da biyan tarar wasu fursunoni da ke zaman gidan yari a cibiyoyin gyaran hali da dama a fadin jihar.

Daraktan kungiyar na kasa, wanda ya zama shugaban kungiyar a Bauchi, Alhaji Bala Ibrahim Sani, ya ce sun dauki wannan mataki na daga cikin ayyukan bukin cika shekaru 48 na JNI a jihar.

Sani ya bayyana cewa an kafa kungiyar agajin ne da nufin gudanar da ayyukan jin kai ga ‘yan Najeriya, ya kuma jaddada aniyar ta na ci gaba da yi wa bil’adama hidima ba tare da banbancin addini ko kabilanci ba.

Shima da ya ke nasa jawabin, fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Dakta Ibrahim Adam Dasina, ya jaddada bukatar matasan musulmi su rika gudanar da sana’o’i daban-daban na samun riba domin dogaro da kai da kuma rage dogaro ga wasu.