
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya nisanta kan sa da wata ƙungiya mai suna Abba Tsaya da Kafar ka, wacce ke rajin ganin an samu sabani tsakanin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da mai gidansa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a kwanakin nan, ana ta jin amon ƙungiyar a gidajen rediyo a Kano, inda ake rade-radin cewa Baffa-Bichi ne ya kafa ta don haifar da rikici tsakanin gwamna Yusuf da Kwankwaso.
Sai dai kuma da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya fito daga wata ganawar sirri da gwamnan Kano a gidan gwamnati a jiya Litinin, Baffa-Bichi ya tabbatar da cewa ba da yawunsa aka kafa wannan ƙungiya.
Ganawar sirrin dai an yi ta ne domin sasanta rikicin siyasa tsakanin Baffa-Bichi da Hamza Maifata, dan takarar ciyaman na ƙaramar hukumar Bichi a zaben ƙananan hukumomi mai zuwa.
A cewar Baffa-Bichi, shi ba matsoraci ba ne domin ba ya boye harkokin sa na siyasa, inda ya kara da cewa da shi ya kafa kungiyar ta Abba Tsaya da Kafar ka da ba zai boye ba.
“Ba da yawu na aka kafa wannan ƙungiya ba. Ba ni na kafata ba. Ni jarumin dan siyasa ne kuma bani da tsoro.
“Da ni na kafa ta ba zan boye ba. Ko One to Tell 10 ma da na kafa ta ai na bayyana kuma kowa ya san Ni na kafata. Saboda haka ban san da wannan ƙungiya ba,” in ji Bichi.
Ya kuma tabbatar da sulhin da gwamna Yusuf ya yi tsakanin sa da Maifata, inda ya jaddada mubaya’ar sa ga gwamnan da kuma bada tabbacin zama lafiya a jam’iyyar.