
Wata mata mai suna Clara Chinwe Deborah Ogo mai shekaru 83 da haihuwa ta tsinci kanta a gidan yari da ke birnin Onitsha a jihar Anambra.
Deborah, wacce take da gidan marayu mai suna Arrow of God Orphanage a Anambra ta shiga hannun jami’an hukumar yaki da safara da cin zarafin dan adam, NAPTIP, wacce ta gurfanar da ita a kotun tarayya da ke Awka.
Matar, wacce tsohuwar soja ce kuma likita, ta na da gidan marayu a Nkwelle-Ezunaka, karamar hukumar Oyi, Anambra da kuma rassa a Legas.
Wani dan jarida mai binciken kwakwaf, Fisayo Soyombo ne ya tona ashirin Deborah bayan zargin safarar ƙananan yara da sayar da su.
Daga nan ne sai Soyombo ya gwada sayen jariri a wajen ta kan Naira miliyan 2 a watan Yuli, lamarin da ya janyo NAPTIP ta fara gudanar da bincike har ya kai ga kama ta.
Ana tuhumar Deborah da laifi guda daya da ya saɓa da sashe na 21 na dokar NAPTIP .
Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta bada belin Deborah ta hanyar bada Naira Miliyan 1.3 da kuma wadanda za su tsaya mata mutum biyu.