Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman Ibn Abdulaziz Alsaoud

Hukumomi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya sun bayar da sanarwar dakile yunkurin kaiwa birnin Riyadh hari a yau da hantsi. Harin dai wanda ake kyautata zaton mayakan Houthi na kasar Yemen da Saudiyyar ke jagorantar yaki da su ne suka kai wannan hari.

Harin dai an nufi wata matattarar jama’a ne a wata unguwa dake dab da birnin riyadh, amma cikin ikon Allah harin bai ci nasara ba, aka kadar da shi. Zamu kawo muku cikakken bayani.