Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Sanusi Rikiji a ranar Asabar ya ja hankalin Gwamnatin tarayya kan batun sha’anin tsaro a jihar da ya tabarbare.

Sanusi Rikiji, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin bayar da agajin gaggawa na jihar, yayi wannan kiran ne a fadar mai martaba Sarkin Zurmi, lokacin da yake magana kan abinda ya faru na kashe sama da mutane 42 da kauyuka 18 dake yankin karamar hukumar mulkin Zurmi.