Home Labarai An kama ɗansandan da ya kaiwa ma’aikacin kamfanin KAEDCO hari da wuƙa a Kaduna

An kama ɗansandan da ya kaiwa ma’aikacin kamfanin KAEDCO hari da wuƙa a Kaduna

0
An kama ɗansandan da ya kaiwa ma’aikacin kamfanin KAEDCO hari da wuƙa a Kaduna

An gano tare da kama wani dansanda mai matsakaicin shekaru da aka dauka a cikin wani faifan bidiyo yana cin zarafin ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDCO).

Daily Trust ta rawaito cewa wanda ake zargin, Aminu Yahaya Bidda, mai muƙamin Sifeton Ƴansanda wanda aka tura ofishin ƴansanda na Tudun Wada da ke cikin birnin Kaduna, an gan shi a faifan bidiyon riƙe da wuka ya na kokarin daɓawa wasu ma’aikatan KAEDCO.

Kamfanin na KAEDCO ya kai rahoto ga rundunar yansandan jihar ta hanyar rubuta koke ga kwamishinan ‘yan sandan.

Koken ya bukaci a kama sufeto Bidda, da bincike, da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifin cin zarafi, yunkurin kisan kai, tsangwama, da kuma tsoratar da ma’aikatan KAEDCO.

KAEDCO, a wata sanarwa da Abdulazeez Abdullahi, shugaban sashen sadarwa na kamfanin ya fitar, ya bukaci da a mika lamarin ga sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) domin gudanar da cikakken bincike, sannan ya bukaci kwamishinan ‘yan sandan da ya tabbatar da tsaron ma’aikatansa domin su samu damar gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.

Shedun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya kara kamari ne a lokacin da ɗansandan ya fusata ya dauki wuka tare da yunkurin dabawa ma’aikacin KAEDCO amma ma’aikacin ya tsira da kyar.

Sai dai wani mai wucewa da ya yi kokarin shiga tsakani ya samu rauni a kafarsa a yayin rikicin.