Home Labarai An kama ƙasurgumin ɗan neman maza bayan da ya lalata ƙananan yara 19 a Abuja

An kama ƙasurgumin ɗan neman maza bayan da ya lalata ƙananan yara 19 a Abuja

0
An kama ƙasurgumin ɗan neman maza bayan da ya lalata ƙananan yara 19 a Abuja

 

 

Hukumar Kula da Al’umma ta Abuja, SDS, ta kama wani da ake zargin dan luwaɗi ne, wanda ake zargi da lalata ƙananan yara a ƙalla 19 a ƙauyen Karmajiji da ke kan titin filin jirgin sama, Abuja.

Muƙaddashin daraktan kula da jin dadin jama’a na SDS, Sani Amar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Talata a Abuja.

Amar ya ce an kama wanda ake zargin ne bisa umarnin karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu, wacce ke da kishin kare hakkin marasa galihu da kuma yara da mata.

Ya kuma jaddada cewa sakatariyar ci gaban al’umma ta ɗau nauyin tabbatar da kare hakkin marasa galihu da suka haɗa da yara da mata.

“A ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, na samu kira daga ƙauyen Karmajiji cewa wani mutum mai suna Kabiru, wanda aka ruwaito yana son lalata da yara ‘yan kasa da shekaru 12 zuwa kasa.

“Nan da nan na haɗa tawagarmu tare da gudanar da bincike inda muka gano cewa akwai yara sama da 19 da ake zargin ya lalata.

“Hakan ya faru ne a sakamakon ɗaya daga cikin yaran da abin ya shafa wanda aka ce mutumin ya yaudare shi da alewa da lemo ya shiga da shi dakinsa.

“Yayin da ya shiga daki tare da yaron, ya kulle dakin kuma ya yi yunkurin yin amfani da shi da karfin tuwo.

“Yaron ya dage ya ƙi yarda tare da kokawa da mutumin wanda hakan ya sa masu wucewa suka gano cewa akwai matsala a dakin Malam Kabiru (wanda ake zargin), sai suka garzaya cikin dakin aka kama shi,”