Home Labarai An kama malaman bogi a jami’ar Bayero ta Kano

An kama malaman bogi a jami’ar Bayero ta Kano

0
An kama malaman bogi a jami’ar Bayero ta Kano

Jami’an tsaro a jami’ar Bayero dake Kano sun kama wasu mutane guda biyu da suke kiran kansu a matsayin Malaman jami’ar.

An kama mutanen biyu suna siyar da litattafan karatu na bogi ga sabbin ɗaliban ajin farko.

Acewar sanarwar da sakataren yaɗa labarai na jami’ar, Bala Abdullahi ya fitar ya ce waɗanda ake zargin sune: David Iluebe daga jihar Edo da Chike E. Eke daga jihar Delta.

Sanarwar ta bayyana cewa mutanen guda biyu sun shiga ɗakin bada karatu a tsangayar kere-kere inda suka gabatar da kansu ga ɗaliban ajin farko na sashin kan cewa su Malamai ne.

Sanarwar ta ce mutanen sun bayyanawa ɗaliban cewa siyan litattafan ya zama dole ga duk wanda yake son tsallake darasin.

Sai dai jami’an tsaron jami’ar sun samu nasarar kama mutanen wadanda suka amsa laifinsu.

Jami’ar ta ce za a mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin daukar matakan da suka dace inda ta kara da cewa “za mu kara wayar da kan daliban mu kan wannan abu mara dadi da ya faru”.