
Jami’an hukumar tsaron fararen hula da kadarorin gwamnati ta Civil Defence a jihar Adamawa ta kama wani mutum da ake zargi da ya kware wajen siyan kayayyaki da karbar kudi a wajen masu POS yana yi musu transfer ta bogi.
Wanda ake zargin mai suna Jeremiah Stephen, ya ce yana gudanar da harkokinsa a garin Michika da Yola na jihar inda jami’an ofishin hukumar NSCDC na garin Michika suka kama shi.
Mai magana da yawun rundunar na jihar Adamawa, DSC Amidu Nyako ya bayyana cewa, Stephen mai shekaru 24 ya amsa laifinsa inda ya tabbatar da cewa ya damfari mutane da dama.
Hukumar ta NSCDC ta shawarci masu POS da ‘yan kasuwa da su dinga duba kudaden da aka turo musu kafin bayar da kaya ko tsabar kuɗi.
Hukumar ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Daily Post