Dr. Aliyu Tilde
Yanzu na gama shan abarba a Zungeru Road inda ake min gyarar mota. Zanne kan benchi, bayan na sha abarba ta kai min karo, sai na tambayi mai-tallar abarbar ta nawa na sha.
Ya ce, “Ta Naira dari biyu.
Sai na sake habata, na ce: “Malam, yar wannan din?”
Ya ce, “Kwarai kuwa.”
Sai na yi ajiyar zuciya, na tambaye shi: “Hala kai Bakano ne dan na ganka da uku-uku a kuncinka.”
Ya ce, “E. Bakano, cikakkensa.”
Na ce, “Haba. Ai ba mamaki. Don tsakanin Bakano da Inyamuri ban san wanda ya fi son kudi ba. Kanawa dai mun san su da sane.”
Sai ya yi wuf, ya ce, “A da ne, ranka ya dade.”
Na ce, “To ai ka ji. Da kuka daina sane shi ne kuka koma satar mota ba?”
Ya ce, “To ai an gudu ba a tsira ba ke nan.”
Na ce, “Ni tun 1978, shekara arba’in ke nan, in na je Kasuwar Kurmi, hannu na dafe yake da aljihuna.”
Kafin in gama bayani, sai mai-abarba ya ce, “Wallahi ni ma a nan suka koya min hankali.”
Na ce, “Ya aka yi?”
Ya ce, “Ai da na je da gwaiba shekarun baya sai suka kira ni kamar za su saya. Suka mamaye ni wai bari su taya ni saukewa. Ashe yayin da wasu suke kama min tire, wani ya sa hannu a aljihun kirjina ya zare dan cinikin da na yi.”
Na tuntsire da dariya, na tambaye shi: “To ya ka yi?”
Ya ce, “Na bar su da Allah.”
Na ce, “Tab. “Ka ce dara ta ci gida.”
Nan na ba shi labarin yadda Kanawa suka sace wa yarona, Omer, mota a Farm Centre shekaru uku da suka wuce. Ya je masallacin juma’a latti, sai garin sauri don ya riski raka’ar karshe bai kulle kuloch ba. Ana idar da sallah ya yi sauri ya dawo wajen mota, sai ya ga wayam. Har yau! Kan ka ce kwabo an kai ta Sabongari an sassare ta wajen su Kachikwu.
Nan dai hirarmu ta kare da mai-abarba. Na ciro N200 zan mika mar sai na ce, “Ko za ka yi sadaka da dari daya ne, in baka dari kawai?”
Ya dara, ya ce, “A yi haka, yallabai?”
Na ce, “Ato. Ai kanawa ba sa sadaka. Mabaratansu ma fata suke baki Zagezagi su shigo birni don su sami na kashewa. Ka san sadaka sai masu ilimi, ba yan sane ba.”
Ya ciccibi tiren abarbarsa ya dora a ka. Ban tallafe shi ba, kalen ya yi tsammani zan zare mar aljihu yadda aka taba mar a Kasuwar Kurmi.
Abin na Kanawa da ban mamaki.