Malam Salihu Sagir Takai da ya yiwa jam’yun ANPP da PDP takarar Gwamna a zabukan 2011 da 2015 ya yanki takardar sake neman kujerar Gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Wannan shi ne karo na uku da Malam Salihu Sagir Takai yake neman takarar Gwamnan jihar Kano. A baya yayi takara a 2011 inda Sanata Kwankwaso ya samu galaba a zaben da tazara ‘yar kadan.

Sai dai a zaben 2015 Malam Salihu Sagir Takai ya kuma shan Kaye a hannun Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, masu sharhin Siyasa a jihar Kano na ganin cewar a wannan karon Malam Salihu Sagir Takai na Iya samun galaba akan Gwamna mai ci Ganduje, idan har PDP ta amince ya bashi takara.

A zaben bana dai za a samu gagarumin canji a jihar ta Kano, kasancewar tsaffin Gwamnonin jihar guda biyu Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da dumbin magoya baya, kuma na tare da jam’iyyar ta PDP.

Haduwar Shekarau da Kwankwaso a cikin inuwar jam’iyyar PDP babbar barazana ce ga sake komawar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, kasancewar su duka tsaffin Gwamnonin na da dumbin magoya bayan da zasu iya kayar da Gwamna Ganduje.

Daman dai ba abin mamaki bane a jihar Kano a kayar da Gwamna kai ci a yukurinsa na sake komawa, domin ko a 2003 Malam Shekarau ya kayar da Gwamna mai ci Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da shima Malam Shekarau yana Gwamna Kwankwaso ya kayar da dantakararsa Malam Salihu Sagir Takai.

A wannan zaben na 2019, jihar Kano na databank cikin inda za a fafata sosai, inda tsaffin Gwamonin jihar biyu zasu kalubalanci Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje. Shin ko PDP zata samu Nasara a jihar Kano? Lokaci je zai tabbatar da hakan.