
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Karamar Hukumar Fagge, Mohammed Bello Shehu, ya kaddamar da daukar nauyin yi wa yara su dubu daya kaciya kyauta.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ɗan majalisar, wanda aka fi sani da MB Shehu, ya ɗauki nauyin yin kaciyar ne ga yara a dukkanin mazabu 11 na mazabar tarayya ta Fagge.
Da ya ke shaida wa Daily Nigerian Hausa dalilin da ya sanya shi ya kirkiro da shirin, irinsa na farko a jihar, MB Shehu ya ce ya yi hakan ne domin ya saukakawa iyaye biyan kudin yin kaciya.
A cewar sa, ya ga dacewar ya dauki nauyin yin ka iyar ta gamayya bayan da wani mutum ya zo ya roke shi da ya taimaka ya biya masa kuɗin kaciyar ƴaƴansu guda uku.
Dan Majalisar ya kara da cewa “wannan ne ya sanya na yi tunanin cewa akwai iyaye da yawa irin wannan mutumin da su ke da ƴaƴan da za a yi wa magoya amma basu da kudin biya, shi yasa na yi tunanin yin kaciyar ga yara dubu domin saukakawa mahaifan su,” in ji MB Shehu.
Ya ce tuni ma an fara aikin yin kaciyar a yau Lahadi, inda ya kara da cewa za a bi duk mazabun Fagge a yi wa wadanda suka cike fom din da aka raba domin samun gurbin yin kaciyar.
“An nuna min a bidiyo yadda mutane aka cika. Don 1000 muka ranar, sun kare amma har yanzu zuwa nema a ke. Mun yi hakan ne don saukakawa iyaye,” in ji MB Shehu.
Ya kara da cewa tun shigar da ofis a matsayin ɗan majalisar tarayya, ya na ta amfani da kudin aljihun sa wajen aiwatar da aiyukan ci gaba ga al’ummar sa.
“Daga hawa na zuwa yanzu, na kashe sama da Naira miliyan 200 wajen yi wa al’ummar Fagge aiki. Ko a bangaren ilimi ma Naira miliyan 58 na kashe wajen biyan kudin NECO da kudin makaranta na yan gana da sakandare.
“Na bada taimako a ɓangaren lafiya da jari ga mata da matasa da sauransu. Yanzu dai muna jiran a fitar da kasafin kudi na bana, a nan ne za mu baro aiyukan ci gaba sosai ga al’ummar mu,” in ji shi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ana baiwa ko wanne yaro magunguna da allurori da kudi bayan an kammala masa kaciyar.