Home Labarai A karon farko Amurka ta kai wa Gaza kayan agaji a ta sama

A karon farko Amurka ta kai wa Gaza kayan agaji a ta sama

0
A karon farko Amurka ta kai wa Gaza kayan agaji a ta sama

Amurka ta kai agaji na farko a zirin Gaza, inda jirage guda uku suka harba wa mutane sama 30,000 abinci daga sama.

Wannan shi ne karon farko da Amurka ta kai agaji zuwa Gaza tare da haɗin gwiwar sojojin saman ƙasar Jordan, bayan sanarwar da shugaba Joe Biden ya yi na cewa za su kai agaji.

Shugaban wata fitacciyar ƙungiyar agaji ya shaida wa BBC cewa akwai tsananin yunwa a arewacin Gaza.

Akalla mutum 112 ne suka mutu yayin da jama’a lokacin da jama’a suka yi ribibin karɓar kayan agaji a wajen birnin Gaza ranar Alhamis.

Hamas dai na zargin waɗanda suka kawo agajin da kisan mutanen. Isra’ila ta musanta hakan kuma ta ce tana gudanar da bincike.

Jirgin na farko na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da wani babban jami’in Amurka ya ce tsarin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako shida a Gaza na ƙasa.