
Wani da ake zargi da satar babur ya gamu da ajalinsa a unguwar Apalara da ke Karamar Hukumar Ilorin ta yamma.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Daily Trust cewa an cafke wanda ake zargin ne bayan ya yi yunƙurin daɓawa ɗan achaɓar da ya ɗauko shi wuƙa a baya.
“Duk sai suka fadi ƙasa, inda wanda ake zargin yayi yunƙurin guduwa da babar din.
“Daga nan ne jama’a su ka bishi har su ka cimma sa, inda su ka riƙa jibgarsa har sai da ya ce ga garin ku nan,” in ji shaidun gani da idon.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi ta tabbatar da lamarin, inda ta ce wanda ake zargin ya mutu ne bayan an garzaya da shi asibiti.