Home Labarai An kashe ƙarin sojin Isra’ila biyu a Gaza

An kashe ƙarin sojin Isra’ila biyu a Gaza

0
An kashe ƙarin sojin Isra’ila biyu a Gaza

Isra’ila ta fitar da sunayen ƙarin sojoji biyu da aka kashe a faɗan da take gwabzawa da mayaƙan Hamas a Gaza.

Sojojin da aka kashen su ne Isahar Natathan mai shekara 28 da kuma Itay Shoam mai shekara 21.

Hakan na nufin Isra’ila ta rasa sojojinta 44 a yaƙin na Gaza.

Isra’ilar ta kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin sojojin nata ya samu mummunan rauni a faɗan da aka gwabza ranar Lahadi.

BBC Hausa