
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, ACF ta nuna rashin jin daɗi bisa abinda ta ke zargi na nuna rashin damuwa da gwamnonin Jihohin Arewa ke yi ga garuruwan da ƴan ta’adda ke kaiwa hare-hare a yankin.
A wata sanarwa da kakakin ACF ɗin, Emmanuel Yawe ya fitar a yau Litinin a Kaduna, ƙungiyar ta nuna cewa gwamnonin Arewa ba sa nuna tausayi ga waɗanda kashe-kashen ya ke shafa.
ACF ta ƙara da cewa gwamnonin Arewa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun baiyana kansu a matsayin waɗanda ba su damu da talakawa ba sai dai kawai sun fi damuwa da iyalin su da sauran harkokin gabansu.
“Shugaban ƙasa da gwamnonin Arewa na nuna mana cewa sun fi damuwa da rayuwarsu da kuma ta iyalansu da kuma ƴan uwansu da harkokin ofisoshin su,” in ji ACF.
ACF ta ƙara da cewa bayan gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, tsakanin shugaban ƙasa da gwamnonin arewa babu wanda ya ke damuwa da ya ziyarci garuruwan da yan ta’adda ke kai hare-hare domin yin jaje.
“Sabo da haka ACF na nuna bakin cikin ta da ɓacin ranta a kan abinda ta ke ganin cewa wannan kashe-kashen ba zai ƙare ba a Arewa.
“Abinda ya faru a Giwa a Kaduna yanzu, inda a ka kashe mutane 38 kisan gilla. Babu wani abu da ya hana Shugaban ƙasa da gwamnonin Arewa su ziyarci guraren da a ka yi kisan.
“Amma ya nuna mana cewa shi bai ga ma dacewar ya kai ziyarar. Amma dama kamar yadda ya ke nunawa, babu wani wanda zai iya kai ziyarar jaje sai Zulum,”