
Mutane huɗu ne a ke tsammanin sun mutu da suka haɗa da ƴan kungiyar asiri daban-daban a Unguwar Olunlade, Ilorin, a lokacin da ake gudanar da bukukuwan bikin ranar 8 ga watan Agusta (8/8).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, a jiya Talata a Ilorin.
Ya bayyana cewa alƙaluman hukuma sun nuna cewa mutane biyu ne kawai su ka mutu, inda ya ƙara da cewa amma mutanen yankin sun ce Mutane 4 ne su ka mutu a yayin harin ramuwar gayya da ga kungiyoyin asiri daban-daban.
Sai dai ka kakakin ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyu a yayin da lamarin ya faru.
Okasanmi ya ce: “Mutane biyu ne kawai aka kashe a bikin 8/8 da kungiyoyin asiri suka y, ba mutane hudu ba kamar yadda wasu mutane suka yi ta yaɗa wa.
“Mutum daya ya mutu a wurin rikicin a Olunlade yayin da daya kuma aka ruwaito ya mutu daga baya a asibiti.”
Kakakin ya ce mai yiwuwa abin da ya haifar da rikicin shi ne bikin ranar 8 ga watan Agusta, kuma kungiyoyin asiri daban-daban ne su ka gudanar da bukukuwan ranar a wurare da dama a cikin garin.