Fusatattun gamagarin matasa

Rahotanni daga jihar Taraba sun ce an kashe a ƙalla mutum shida a garin Ɗan Anacha sakamakon fusatar wasu gamagarin matasa a yankin karamar hukumar Gassol. Bayanai sun ce, matasan sun fusata ne har suka dauki doka a hannun sakamakon yin batanci ga addinin Musulunci da kuma Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam da wani mutum yayi a wata mashaya.

Wani matashi da abin ya faru akan idonsa mai suna Habu Ɗan Anacha ya shaidawa DAILY NIGERIAN ta wayar tangaraho cewar “wani ɗan asalin ƙabilar Tibi ne a wata mashaya, bayan yasha barasa yayi tatul ya zagi Manzon Allah SAW a bainar jama’a.

Wannan ce ta harzuƙa wasu Musulmi dake wajen, abin da ya kai wasu fusatattun matasa suka ɗauki doka a hannu, a sanadiyar hakan wasu mutum shida suka hallaka. Shi dai mashayin ɗan ƙabilar Tivi bayan da ya shawu ne, taƙaddama ta barke tsakaninsa da wani a wajen, daga nan ya fara yin munanan kalamai akan addininMusulunci da kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam”.

Bayan wannan ‘yar hatsaniya ne, ‘yan sanda suka garzayo domin kwantar da tarzoma, inda suka kama mutumin ɗan ƙabilar Tibi suka yi awon gaba da shi. Wannan ce ta sanya ‘yan uwansa ‘yan kabilar Tibi suka garzaya caji ofis na ‘yan sandan domin neman belinsa, abin da ‘yan sanda suka ce ba zata saɓu ba.

Daga bisani ne kuma, matasan ‘yan ƙabilar Tibi suka shiga tayar da hayaniya bayan da aka hana su belin ɗan uwan nasu, sun shiga bankawa shagunan mutane wuta, da kakkarya turakun lantarki na kan titi da sauran ayyukan ta’addanci. Inda hakan yayi sanadiyar mutuwar wasu mutum shida nan take.

Haka nan, wata mata mai maƙotaka da wajen Lami Danladi, lamarin ya haifar da turmutsutsi a gurare da dama, inda mutane suka dinga gudu suna barin kayan sana’arsu domin ceton rayukansu.

Tuni dai hukumomi suka kafa dokar ta-baci a yankin, babu shiga babu fita, domin shawo kan wannan hargitsi. David Misal, kakakin rundunar ‘yan sabda ta jihar Taraba, tuni ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

Ya shaidawa wakilnmu ta waya cewar, tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta tura jami’an tsaro yankin domin dawo da doka da oda. Ya ƙara da cewar, “a yayin da nake magana da kai yanzu haka, akwai tarin jami’an tsaro a yankin domin tabbatar da wani mummunan abu bai sake faruwa ba”.

Sai dai yace ba zai iya tabbatar da ko adadin mutum nawa ne suka rasa rayukansu a sakamakon wannan tashin hankali ba. Amma dai ya tabbatar da cewar, tuni suka shiga bincike dan tabbatar da musabbabin faruwar lamarin da kuma gano ko mutum nawa ne suka rasa rayukansu.