29.1 C
Abuja
Friday, April 19, 2024

Kasuwar Baje-kolin Kaduna: Buhari, El-Rufai da KADCCIMA sun karrama Dangote

Must read

Shugaban Ƙasaasa Muhammadu Buhari da mai masaukin baƙi,  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun yaba wa shugaban Rukunin Kanfanunuwan Dangote, Alhaji Aliko Dangote, bisa ƙwarin gwiwar sa wajen haɓɓaka kasuwanci da kuma taimakawa al’ummar kasar nan.
Buhari da El-Rufai sun baiyana hakan ne a wajen bikin baje-koli na Kaduna karo na 43, wanda shugaban ƙasar ya ƙaddamar a karshen mako.
Cibiyar da ts shirya bikin baje kolin, Cibiyar Kasuwanci, Ma’adinai da Noma ta jihar Kaduna wato (KADCCIMA) ta baiyana Dangote a matsayin wanda ya fi bayar da gudunmowa ga cigaban tattalin arziki da kuma gudanar da aiyukan jin kai ga al’umma ta karkashin Gidauniya Aliko Dangote.
Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo, ya kuma ziyarci rumfar Dangote inda ya ce kasar nan na godiya da irin tallafin da rukunin Kamfanoni Dangote ke baiwa al’ummar Nijeriya.
 Ya baiyana Aliko Dangote a matsayin abokinsa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya, tallafawa ayyukan gwamnati da na zamantakewa.
 Kamfanin Dangote shi ne mafi girma wajen daukar nauyin Kasuwar Baje-kolin ta kasa da kasa a Kaduna karo na 43 da a yanzu haka ta ke gudana mai taken: Sake damarar bunkasa tattalin arzikin Najeriya don yayi dai-dai dana sauka kasashen duniya.

More articles

Latest article