Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama Abuja, ta zartar da hukuncindauri na shekaru 12 a gidan kurkuku ba tare da zabin tara ba.

Shugaban hukumar kula da aukin Hajji ta kas, Abdullahi Mukhtar ne ya maka IG Wala a gaban kuliya kan zargunda yayi na bata masa suna da Wala ke yi a shafinsa na Facebook.

Kotun ta samu IG Wala da laifin baa suna da zargi mara tushe ga Shugaban hukumar, dan haka ta tasa keyarsa zuwa gidan maza na shekaru 12 batare dazabin biyan tara ba.