
Kwamishinan Ƴansanda na jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya bayar da tabbacin cewa an haɗa hannu waje guda domin kawo karshen matsalar yan bindiga da garkuwa da mutane nan da watanni uku a jihar.
Yusuf ya ba da wannan tabbacin ne a jiya Alhamis yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya da ta ƴan kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki.
Yayin da yake kira ga shugabannin kwadagon da su yi watsi da shirin yajin aikin, Mista Kolo ya ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru don ganin ta biya dukkanin bukatun kungiyoyin.
“Abin da wannan gwamnati ke bukata a yanzu shi ne addu’a. Mutane suna kira da a dauki matakin yajin aiki nan da can. Hatta ’yan kwadagon sun so shiga yajin aikin, amma sun saurare ni bayan na yi roko gare su, suka dakatar da barazanar tafiya yajin aiki.
“idan duk ku a nan ba ku tashi tsaye ba, za ku durkusar da jihar. ‘Yan fashin na can kuma sun ki barin kowa ya yi noma. Ko barci ba na iya yi. Ina can ina ta kiran DPOs da kwamandojin yanki don magance matsalar.
“Kuma da yardar Allah nan da watanni uku masu zuwa za a shawo kan dukkan matsalolin. Gwamnatin tarayya da ta jihohi sun samar da dukkan hanyoyi domin kawo karshen tada kayar bayan. Don haka mu marawa gwamnati baya domin kawo karshen tada kayar baya, mu manta da shiga yajin aikin,” inji shi.
Da yake mayar da martani, Shugaban Kungiyar Kwadago na Zamfara, Saidu Mudi, ya ce har yanzu kungiyar ba ta samu umarnin janye yajin aikin daga hukumominta na kasa ba, don haka za su ci gaba da yajin aikin.