Malam Nazeer Nuhu Muhammad
Wani matashi mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a shafinsa na Facebook ya wallafa wani kira zuwa ga Gwamnatin Kano kan yadda ake cefanar da filayen Masallatai barkatai a cikin garin kano. Matashin ya ja hankalin gwamnatin Kano kan shirin ta na sayar da katangar da ta kewaye masallacin Juma na Fagge da aka fi sani da Masallacin Waje.
Matashi Nazeer Nuhu Muhammad ya wallafa wannan kira nasa ne ga Gwamnatin Kano da masu janragamar hukumomin da ke kula da sha’anin filaye a jihar Kano, ga yadda ya wallafa kiran a shafinsa:
“A Nigeria Gwamnati babu ruwan ta da Addini, bai kamati a ce ta kwallafa ido akan dukiya mallakin addini don biyan bukatar kai ba. Irin wannan filaye a tarihi ba gwamnati ke bada su ba ko dai alummar gari su sadaukar da filayen su don yin masallaci ko maqabarta ko masarauta ta bayar kyauta.
Gwamnatin Kano ta sayar da Katangar Massalacin Fagge (massalacin waje) yanzu suna gine Masalallcin idi duka don sama wa kansu kudaden shiga ba wai don samar wa masallacin kudi don dogaro da kai ba.
Massalcin waje shi ne masallaci mafi girma a Kano, saboda girman sa amma yanzu Gwamnati ta doke katangar an maida ita ciki wanda ana kyautat zaton nan ma shaguna zaayi.
Wannan masallaci na waje (Masallacin Fagge) Gwamnati ba ruwanta dashi duk da kwace da ake wa mutane saboda duhun ciyawa rashin wutar lantarki da futulun haskaka wuri da zaizayar qasa da ya ke fama dashi abin takaicin sai ka shiga masallacin kaga yadda carpet ya zama kamar an watsa masa kasa saboda datti dukkan bangwayen masallacin yana saman masallacin da damuna yana zuba  fankoki basa yi zaka sha mamaki in aka ce maka wannan masallaci a kano ya ke saboda yadda ya lalace duk da sunan marigayi Mai martaba Abdullahi Bayero gare shi amma ya rasa gata daga Masarauta ballantana Gwamnati walau mutanen gari.
Ba gina shaguna ne abin takaici ba  kudin wa za’a ba ? Shin shagunan na masallacin ne ko na gwamnati ne ko na wadan da suka biya kudi ne? Me zaa ringa yiwa masalaltan kano duk shekara da kudin?
Ya kamata Ali Baba ka sani Shaguna ko Hotel a kasar saudiya in Gwamnati ce ta ke da su to masallacin akewa hidima da kudin kuma gwamnatin  qasar saudiya ita ke tafi kar da Harkokin addini a qasar ta.
Zamanin Gwamnatin Mallam Ibrahim shekarau ya fito da tsari na yiwa Limamai da Ladanai Allowance amma da kuka zo ku ka soke saboda ba ruwan ku da addini.
Kun Gine hanyoyi, kun gine filayen makarantu, kun gine Masallatai saura maqabarta duka ku dai ku sa a aljihun ku. Allah yana nann a madakata.”