
Mai ɗakin shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kaɗuwarta kan mutuwar Nabeeha Al-Kadriya, da ƴan bindiga suka halaka.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Sanata Oluremi ta bayyana mutuwar Nabeeha a matsayin rashi mai matuƙar sosa zuciya inda kuma ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar.
Sanata Oluremi ta kuma buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kansu wajen yin addu’oi da za su kai ga sakin ƴan’uwan Nabeeha, waɗanda har yanzu ke a hannun masu garkuwa.
Da take magana kan ƙaruwar matsalar tsaro da sace-sacen jama’a, Oluremi ta yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen hana satar jama’a su kuma yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ƴan’uwan Nabeeha.
A ranar 2 ga watan Janairu Nabeeha da ƴan’uwanta suka faɗa hannun ƴan bindiga a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Mahaifinsu Mansoor Al-Kadriyar, wanda shi ma ya shiga hannun masu garkuwar daga bisani sun sake shi domin ya dawo gida a haɗa kuɗin fansar ƴaƴansa.
BBC Hausa