
Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da sanya dokar hana fita a garin Sabon Birni da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto a daidai lokacin da matasa suka fara zanga-zanga kan kisan Hakimin Gatawa, Isa Muhammad Bawa.
Kakakin rundunar ƴansandan, ASP Ahmed Rufa’i ya ce babu zirga-zirga a yankin tsakanin karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma har sai an samu sanarwa.
Ya ce an dauki matakin ne domin dawo da doka da oda a yankin.
Daily Trust ta rawaito cewa matasa daruruwa ne suka cika wasu manyan titunan yankin tare da cinna wuta a wasu wajaje.
An ce sun kona sakatariyar jam’iyyar APC ta karamar hukumar da wata kotu.
Haka kuma sun kutsa cikin wani rumbu tare da lalata takin zamani.
Turakin Gobir, wanda dan Hakimin da aka kashe ne ya shaida wa Daily Trust cewa, an fara samun zaman lafiya sakamakon taimakon jami’an tsaro a yankin.