Gwamnan jihar Kaduna Mallam nasiru el-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya bayyana a shafinsa na Facebook The Governor Kaduna State cewar ba zasu saurarawa duk wata matsin lamba akan kudurinsu na korar gurbatattun Malaman Firamare a jihar ba.

Gwamnan ya bayyanaa cewar, sunyi rantsuwa da Allah da kuma littafi mai tsarki akan cewar, zasu yi gaskiya da Adalci. Dan haka dole nee su aiwatar da wannan kuduri ko da kuwa bai yiwa al’umma dadi ba.

“Mu ba mutane bane da muke tsoron kalubale ko wanne iri, zamu mayar da martanin da ya dace ne, ina amfanin badi babu rai? Idan har zamu bayar da kai bori ya hau? Babu wani wanda ya isa, ya tursasa mu kaucewa hanyar gaskiya ko saba rantsuwar da muka yi da littafi mai tsarki”

“Ci gaba da tafiya tare da Malaman da ba zasu iya koyar da ingantaccen ilimi a makarantun gwamnati cin amanar rantsuwar da muka yi ne, dan haka mu kuma ba zamu ci amanar rantsuwarmu ba, sabida matsin lamba”

“Zamu dauki sababbin Malaman Firamare a Kaduna wadan da suka cancanta su koyar, ba zamu cigaba da biyan gurbatattun Malamai albashi ba” Inji Gwamna Nasiru el-Rufai.